12 Maris 2020 - 05:03
Iran: Shugaban Yaki Da Cutar Corona Ya Ce Zama A Gida Ya Yi Amfani A Kasar Sin

Shugaban kwamitin Yaki Da Cutar Corona a nan kasar Iran ya bayyana cewa, tsarin zama a cikin gida da kuma hana mutane shiga da fita daga wasu garuruwa ya amfana a wajin yakar cutar Corona a kasar Cana, ya kuma yi fatan a aiwatar da wannan tsarin a birnin Qum na kasar don kawo karshen cutar.

(ABNA24.com) Shugaban kwamitin Yaki Da Cutar Corona a nan kasar Iran ya bayyana cewa, tsarin zama a cikin gida da kuma hana mutane shiga da fita daga wasu garuruwa ya amfana a wajin yakar cutar Corona a kasar Cana, ya kuma yi fatan a aiwatar da wannan tsarin a birnin Qum na kasar don kawo karshen cutar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Sayyeed Mahdi Mukaddisi yan fadar haka. Ya kuma kara da cewa, da an dauki irin wannan mataki na killace birnin Qom tun bayan bullar cutar, da an takaita barnan da take yi.

Muqaddisi ya kara da cewa har yanzun yakamata kwamitin yaki da cutar ta Corona ya yi tunanin daukar wannan matakin a kan wasu garuruwa a kasar don gaggauta kawo karshen annobar.

Daga karshe shugaban kwamitin yaki da cutar ta Corona kuma dan majalisa mai wakilatar lardin Markazi ya yabawa jami’an jinya wadanda suke gaba-gaba a wannan yakin, ya kuma kara da cewa rufe makarantu da kuma amfani da matakan da jami’an kiwon lafiya suka bayar ya taimaka wajen rage yaduwar cutar ya zuwa yanzu, amma akwai bukatar a kara daukar wasu Karin matakan.



/129